Dan takarar jam'iyyar APC Ahmad Babba-Kaita ya doke dan uwansa Kabir Babba-Kaita na PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar dattawa da aka gudanar a Katsina ta arewa a ranar Asabar.
Hukumar zabe ta ce Ahmad Babba-Kaita na APC ya samu kuri'u 224,607, yayin da Kabir Babba Kaita na PDP ya samu kuri'u 59,724.
'Yan uwan biyu sun fafata ne domin cike gurbin marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu a farkon watan Afrilun bana.
An dai gudanar da zaben lafiya ba tare wani tashi hankali ba duk da zaben na 'yan gida daya ya ja hankali a Katsina da ma Najeriya baki daya.
Hukumar zaben a Najeriya ta gudanar da zaben cike gurbi na 'yan majalisa a jihohi guda hudu da suka kunshi Katsina da Kogi da Bauchi ta kudu jihar Cross Rivers.
Sai dai kuma zaben jihar Kogi ya bar baya da kura inda rahotanni suka sun nuna cewar an samu matsalar satar akwatunan zabe da har ya janyo rasa rayuka.
Rikici da Matsalar satar akwatunan zabe da sayen kuri'u ne rahotanni suka ce suka mamaye zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya da aka gudanar a jihar Kogi.
Rahotannin sun ce mutum biyu aka kashe a lokacin da ake zaben cike gurbin na dan majalisar Tarayya da ke wakiltar Lokoja/Kogi da Koton Karfe.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN cewa an kashe mutanen biyu ne yayin da suka yi kokarin satar akwatunan zabe.
Akwai runfunan zaben da kuma rahotanni suka ce 'yan bangar siyasa sun hana gudanar da zaben.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)