olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Jami'an Tsaro Sun Hana Sanatoci Shiga Majalisa!



Jami'an tsaron najeriya na farin kaya (DSS) sun hana wasu 'yan majalisar dattawan kasar shiga zauren majalisar da safiyar talata.

Jami'an, da suka ce sun tare hanyar shiga zauren ne bisa umarnin da aka ba su 'daga sama', sun kyale 'yan majalisar sun shiga zauren majalisar daga baya.

Rahotanni dai suna zargin cewar hana 'yan majalisar shiga na da alaka da yunkurin tsige shugaban majalisar, Bukola Saraki. 

Wannan lamari na aukuwane a lokacin da ake cigaba da takun saka tsakanin shugaban majalisar da wadanda sukeso su tsigeshi.

Related Posts

Related Posts

Post a Comment