olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Man/U Batason Sayar Da Pogbo, Lukaku Zai Daina Bugawa Kasar Sa (Belgium)

Pogba ya koma man u ne a shekarar 2016 akan fam miliyan 89

Manchester United ta ce ba za ta sayar da dan wasan tsakiyarta dan Faransa, Paul Pogba, wanda yake son komawa Barcelonain ji jaridar(Sun).

Ita kuwajaridarMirror ta ce Arsenal tana da kwarin gwiwar ci gaba da rike dan wasa tsakiyar Wales, Aaron Ramsey, mai shekara 27, duk da cewa Barcelonada Lazio suna son dan wasan.

KocinTottenham Mauricio Pochettino ya shaida wa (Sky Sportscewa yana ganin wasu 'yan wasan za su bar kulob din kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa duk da cewa Spurs ba ta sayi ko dan wasa daya ba a wannan lokacin bazarar.

Moussa sissoko

Amma kuma (Talksport) ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Tottenham,dan Faransa, Moussa Sissoko, mai shekara 29, ya shaida wa magoya bayan kulob din cewa shi zai tsaya a kungiyar.

Pochettino ya kuma ce yana shirin kasancewa da Tottenham na tsawon lokaci bayan ya samu damar koma wa Real Madrid, ko Chelsea a kakar da ta gabata, kamar yadda jaridar (Mirror)ta ruwaito.

Chelsea ta tattauna da dan wasan gaban kungiyarLyon,Nabil Fekir, mai shekara 25, a lokacin bazara, amma a lokacin bazara ta ki sayen dan kasar, Faransan, a cewar (Goal).

Yaya toure

Ita kuma jaridar (Sunta ambato kocin West Ham, Manuel Pellegrini, yana cewa kungiyarsa ba za ta sayi dan wasan tsakiyar Ivory Coast, Yaya Toure, mai shekara 35, wanda ya kasance ba shi da kulob, tun bayan da ya bar Manchester City.

Dan wasan gaban Manchester United dan kasar Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 25, ya ce yana son ya daina buga wa kasarsa kwallon bayan kammala gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta Euro, wadda za a yi a shekarar 2020, in ji (Business Insider).

Real Madrid ba ta ji dadin cewa Inter Milan ta tuntubi dan wasanta na tsakiya dan kasar Croatia, mai shekara 32, Luka Modric, ba tare da fara tuntubar kulob dinsa ba, a cewar (Mundo Deportivo).


Related Posts

Related Posts

Post a Comment