olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Wani Mutum yana tafiya a kasa daga Lagos zuwa Abuja domin nuna adawarsa ga takarar Shugaba Buhari !


Malam Isa Muhammad Munkaila wanda yace yana adawa da sake tsayawar Shugaba Muhammad Buhari takara ya fara tattaki daga Lagos zuwa Abuja jiya Alhamis kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. 

Jaridar Vanguard ta yanar gizo ta jiya Alhamis ta rubuta rahoton cewa wani mutum mai suna Malam Isa Muhammad Munkaila dan asalin jihar Borno dake adawa da sake tsayawar Shugaba Muhammad Buhari takara ya soma tafiya a kasa daga Lagos zuwa Abuja.

Isa Muhammad Munkaila ya dauki matakin ne a madadin matasan Nigeria da ya ce an yi masu alkawarin ayyuka da zara Buhari ya zama shugaban kasa. Saboda haka suka hada kai suka zabi shugaban, amma kaico, ya ba su kunya. Maimakon kirkiro ayyuka miliyan uku kamar yadda ya yi alkawari cikin shekaru uku abun da aka samu basu wuce 500,000 ba.

Malam Isa Muhammad Munkaila ya ce babu wanda ya zuga shi ko tunzura shi ya dauki matakin da ya dauka. Ya ce yana yi ne ba domin kudi ba, yana da nashi kudin. Kazalika ba ya cikin wata jam’iyyar siyasa. Yana wakiltar matasan Nigeria ne.

Related Posts

Related Posts

Post a Comment