Dan Sarki chapter 2
Ta kalleshi ta ce Aryan kayi hakuri tasamaka Kaji, yau kafafuna ke ciwo. Ya dago a hanzarce ya kali gefen da mahaifiyar tashi take kishingide wanda tunda yashigo yake kallon wayar hannunshi ya matzo kusa da ita yana fadin the only ciwon kafafunnan yana matsa miki now a days koxamu fita dakene abroad a dubaki tayi murmushi ta kalleshi tace haba yarima daga ciwon kafa sai fita kasar waje ai bai kai can ba kaji yace if u insist,sai alokacin mahaifiyar tashi tafahimci cewa har yanxu Balkisu tana nan tsaye sai tace yarima akawo abincin ko yadago yakalle ta kafin yace the only takaimin side dina tace ok Balkisu ki hada kikai mishi side dinshi kinji yar albarka saida yakalleta ya dan karamata harara, ita dai bata masan yanayi ba saboda duniyar tunanin da ta afka sai muryar gimbiyar ce tadawo da ita.
Waye yarima Aryan?
Sunana shi Aryan Ahmad Abubakar saurayi dan shekara 28 aduniya ba fari can bane amma saboda tsabar jindadi yakoma fari mai dukar hankali, ba dogo can kwarai bane bashi da kira irinta zaratan maxa fuskarshi kullum adaure take idan kaga ya saki fuska to agaban iyayenshine baya son hayaniya kokadan, da daya tilo agurin sarki mai darajar daga Ahmad Abubakar da kuma Hajiya Asmau dangata shagwababbe amma Hajiya Asmau tayi kokari gurin ganin dukda gatan da yake samu bai kauce hanya ba irin na wasu yayan masu hannu da shuni yayi karatunshi na nursery, primary harma da secondary acikin Kaduna Zaria inda yawuce London yayi degree dinshi nafarko dana biyu a oxford university yakaran ci medicine indayanxu yaxama kwarraren likitan Mata da yara yadawo Nigerian abisa umurnin mahaifinshi inda ya gina mishi wani babban clinic mai suna *ARYAN SPECIALIST HOSPITAL 💉 💉*
Yanxu haka yana gudanar da aikinshi a asibitin cikin sa'a da nasara sai dai yana fuskantar kalubale daga yanmata saboda suna yawan kawo mishi kansu da batun soyayya idan bai amince ba wasu har soyayyar shanminti suna bukatar suyi amma Allah yatsare shi daga sharrin su.
A gida kuwa yana fuskantar matsi daga iyayen shi akan sunaso yayi aure amma fafur yaki harya kai ga suna zargin koba shida lfy ne suka tambaye shi amma sai yace musu lfy shi kalau shine suka yanke shawarar bashi lokacin inda sarki dakan shi ya zabarma dan lelenshi lokacin wata biyar inda a yanzu yace wata daya da sati biyu daga lokacin da aka dibar mishi.
Yanada aboki guda daya ko ince amini mai suna Fahad, Fahad dane ga wazirin garin halayyarsu daya sai dai shi Fahad yaka sance mai yawan barkwanci da fara'a akasin yarima miskili, Fahad yanada kanne biyu mata Afrah da Farha yan biyu ne masu tsananin kama amma halin su ba daya ba saboda Farha ta kasance maison jama'a mussaman talakawa tana jansu a jiki ita kuma afrah babu wanda ta tsana kamar talaka ko masu kudin bako wa take kulawaba kuma tana masifar son yarima inda take ikrarin zata iyayin komai saboda ta mallaki yarima......

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)