olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Kotu Tayi Shelar Neman Wani Sanata Ruwa A Jallo!!


A ranar Talata ne wata kotun yanki mai daraja ta daya ta bayar da umurnin buga sammacin kama Sanata Hope Uzodinma, wanda ake zargi da bayar da cak din bogi na kudi Naira Miliyan 200

Ana zargin Mista Uzodinma, Sanata mai ci daga mazabar Imo ta Yamma da da kamfanin ‘West, Smiec Engineering da ‘Chemical Construction Company’ da ‘Niger Global Engineering’ da kuma ‘Technical Company’ da bayar da cak na bogi na kudi Naira Miliyan 200.

Mai shari’a, Abdulwahab Mohammed, ya bayar da odan ne bayan da lauyan masu kara, Oluwatosin Ojaomo, inda ya nemi a bayar da odan  a kan wadanda ake zargin.

Mista Ojaomo, lauyan kamfanin Chited Bentures da kuma Chima Akuzie masu karar sun nemi wannan umurnin ne tare da dogara da sashi na 41 da 42 na dokar manyan laifi na kasa.

Ya ce, umurnin ya zama dole saboda wanda ake zargin yana gudun shari’a bayan da aka ba shi sammacin gaiyata a ranar 18 ga watan Satumba 2018.

Ya kuma bayyana  wa kotun cewa, takardar kamun da aka bayar don kama shi an kuma ba shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa don aiwatarwa.

Mista Ojaomo, ya mika wa kotun shaidar cewa ‘yan sanda sun karbi takardar sammamcin amma duk da haka wanda ake zargin ya ci gaba kaucewa shari’a tare da yin kamar babu wani shari’a a kansa.

Haka kuma Mista Ojaomo ya jawo hankalin kotun kan odan wucin gadi na dakatar da ci gaba da shari’ar da wata babbar kotu dake Maitama ta bayar a kan ci gaba da shari’a wadanda ake zargin.

Haka wanda ake zargin ba shi da wani dalilin da zai sa ya ci gaba da kaucewa bayyana a gaban kotun.

Mista Ojaomo ya kuma kara da cewa, wanda ake zargin ya maka alkalin kotun da lauyan masu kara a babban kotun dake Maitama abin dake nuna cewa, a daina wannan shari’ar da ake yi a halin yanzu.

Ida za a iya tuna wa an bayar da hukuncin kamun Uzodinma tare da kuma yanke hukunci daukar cewa yana da laifin har sau ya bayyana a gaban kotun don kare kansa tare da sauran wadanda ake zargin dai dai da sashi na 478 na dokar manyan laifuka na kasa a ranar 18 ga watan Satumba 2018.

Haka kima kamfanin ‘Chited Bentures Ltd’ da Chima Akuzie sun shigar da kara kai tsaye a kan basu cak na kudi na bogi na kudi har Naira Miliyan 200 na bankin UBA, an dai daga ci gaba da sauraran kara har sai ranar 29 ga watan Oktoba 2018.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment