olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Nigeria: Mutane 35 Ne Suka Rasa Ransu Sanadiyyar Gobara!!

Daruruwan mutane ne suka jikkata a gobarar da iskar gas ta haddasa.

Mutum 35 aka tabbatar da mutuwarsu a wata gobara da iskar gas ta haddasa a garin Lafiya na jihar Nassarawa, yayin da wasu daruruwa suka samu rauninka.

Rahotanni sun ce wata tankar dakon gas ce ta kama da wuta a wani gidan man Natson da ke kan babban titin da ya hada Abuja da Arewaci da kuma kudancin kasar.

Kuma wutar ba ta tsaya a anan kadai ba, domin ta kona motocin da ke ajiye a bakin hanya da kuma masu wucewa, da kuma kona shaguna da dama 

Gobarar ta tayar da hankalin mazauna yankin da abin ya shafa.

Mutanen da gobarar ta rutsa dasu sun samu munanan kuna.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment