olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Shin Waye Marigayi Abdullahi Bawa Wase?


Allah ya yi wa jakadan Najeriya a kasar Qatar Malam Bawa Abdullahi Wase rasuwa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Tope Elias-Fatile, ya fitar ranar Asabar ta ce Ambasada Wase ya mutu ne ranar Juma'a da almuru bayan ya yi fama da rashin lafiya.

A cewarsa, za a yi jana'izar sa da misalin karfe bakwai na yamma a agogon Doha, babban birnin Qatar.

"Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya yi matukar kaduwa da jin labarin mutuwar sa sannan ya yi addu'ar Allah ya bai wa iyali da kasa baki daya r hakurin wannan babban rashi," in ji sanarwar.

Bawa Abdullahi Wase fitaccen mai sharhi ne kan harkokin tsaro gabanin nadinsa a matsayin jakadan Najeriya a kasar Qatar.

Yasha yin sharhi a kafafen watsa labarai.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment