olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

An Zargi Ronaldo Da Yiwa Wata Mata Fyade!!



Dan wasan kungiyar Jubentus Cristiano Ronaldo ya musanta zargin da wata mata Ba’amurkiya ta yi masa cewa ya taba yi mata fyade a shekarar 2009 a wani dakin kwana da bata bayyana ba.

Tsohon dan kwallon kungiyoyin Real Madrid da Manchester United ya ce “labarin kanzon kurege ne kuma bashi da tushe ballantana makama.”

A wani faifan bidiyo a shafin sadarwa na Instagram, Ronaldo ya ce: “Suna so ne su tallata kansu ta hanyar amfani da sunansa kuma daman Wannan abu ne wanda  aka saba yiwa manyan mutane.”

Lauyoyin shahararren dan wasan sun ce za su yi karar mujallar kasar Jamus Der Spiegel wadda ta fara ruwaito labarin domin nemawa dan wasan hakkinsa akan kazafin da sukace anyi masa.

Mujallar ta ruwaito matar mai suna, Kathryn Mayorga, tana cewa shahararren dan wasan, mai shekara 33, ya yi mata fyade a wani otel da ke birnin Las Begas na kasar Amurka.

Har ila yau mujallar ta ce Mis Mayorga, mai shekara 34, ta kai kara a wani ofishin ‘yan sanda da ke Las Begas jim kadan bayan faruwar al’amarin sai dai har yanzu babu wani da hukumomi sukayi.

A shekarar 2010, matar ta ce sun cimma yarjejeniyar wajen kotu da Ronaldo, inda ya amince zai biyata dala 375,000, idan ta ki bayyana wa duniya abinda ya faru a tsakaninsu.

Sai dai a wata sanarwa da lauyan dan wasan Christian Schertz ya fitar ta ce: “labarin da mujallar Spiegel ta wallafa ya saba wa doka kuma dole za’ayiwa mujallar hukunci dai dai da laifinta”.

Lauyan ya ce an umarce shi da ya nemi diyyar “bata suna” kan wannan ikirarin da matar take wa dan wasan kuma yana nan ya hada shaidu domin tafiya kotu a biya musu hakkinsu.

Shahararren dan wasan ya koma kungiyar Jubentus ne daga Real Madrid a bana a kan fam miliyan 99.2.

Related Posts

Related Posts

Post a Comment