Babban kotun majistiri da ke garin Minna ta tura wani mai gadi mai suna Michael Itanga dan shekara 55 zuwa gidan kurkuku a bisa zargin ya yi wa wata yarinya karama ‘yar shekara goma fyade da karfin tsiya.
Michael Itang ya kasance a gaban kuliyar ne a sakamakon zargin kamasa da laifin yi wa karamar yarinya fyade sau da yawa.
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Daniel Ikwoche, ya shaida wa kotun cewar wata mai suna Grace Tanko, da take zama a kusa da babban asibitin garin Suleja ne ta kai musu rahoton aukuwar hakan zuwa caji ofis dinsu da ke `A’ Police Dibision Suleja a ranar 3 ga watan Oktaban nan da muke ciki.
ASP Ikwoche ya kara da cewa, mai shigar da korafin ta shaida musu cewar wanda suke zargin mai gadi ne wanda ke gadi a asibitin ‘Christ Rebibal Clinic da ke Suleja, inda take zarginsa da yi wa ‘yarta mai shekaru 10 fyade a cikin dakinsa, ta kuma shaida cewar mai gadin ya maida yarinyarta hawan dalewa, inda ya yi ta mata fyade sau da yawa a cikin dakinsa.
Kamar yadda dan sanda ke bayyanawa, ya ce shi ‘wanda suke zargin’ yana baiwa yarinyar naira 20 zuwa naira 100 gabanin ya aikata danyen aikin nasa.
Ya ce, wannan laifin ya saba wa doka ta 18 ta jihar Neja da ke kan kare hakkin yara ta ‘Child Rights Law’ na shekarar 2010.
A lokacin da aka karanta wa wanda ake zargin laifinsa, ya musanta zargin da ake yi masa.
Mai shigar da kara ya nemi kotun ta dage sauraron shari’ar domin su je su kammala gudanar da bincikensu a kan lamarin.
Da yake yanke hukuncinsa, Alkalin kotun na majistiri, Nasiru Mu’azu ya aike da wanda ake zargin Itang zuwa gidan jarun domin jiran ranar 25 ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraron karar.


![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)