olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Real Madrid Ta Shiga Zawarcin Ramsey!!


Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nuna sha’awarta na siyan dan wasan Arsenal, Aaron Ramsey, wanda kwantaraginsa yakusa karewa a kungiyar.

Ramsey, wanda ya shafe kusan shekaru goma a Arsenal yazo karshen kwantaraginsa a wannan kakar kuma tuni kungiyar tayi masa karin kwantaragi amma kuma har yanzu ba’a cimma matsaya ba.

Dan wasan dai yana bukatar karin albashi a kungiyar irn wanda kungiyar a yanzu take bawa dan wasa Mesut Ozil sai dai bisa dukkanin alamu Arsenal bazata bashi albashi irin na Ozil ba dalilin dayasa shi kuma yake ganin zai bar kungiyar.

Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool dai ta taya dan wasana  kwanakin baya domin siyansa sai dai daga baya Arsenal tace bazata siyar da dan wasan nata ba dan asalin kasar Wales dake yankin birtaniya.

Real Madrid dai tana ganin Ramsey, mai shekaru 27 a duniya zai iya maye mata gurbin dan wasa Toni Kroos dan kasar Jamus ko kuma Luca Modric, wanda a kwanakin baya aka dangantashi da komawa Inter Millan.

Ramsey dai yakoma Arsenal ne daga kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City a lokacin tsohon kociyan kungiyar Arsene Wenger kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin kalubale na FA
Related Posts

Related Posts

Post a Comment