olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

HausaNovel: Dan Sarki Book 1 Chapter [4]


 Dan sarki chapter 4


Tana  shiga sashen tasami Farha zaune suna hira da maman yarima ta zauna suka dan gaisa sai ta tashi ta wuce dakinta dake cikin bangaren na the only. Tunani takeyi mezaisa yarima yace ta rakashi gurin buffday din Afrah bayan tasan yadda Afrah ta tsaneta"ya Allah ka tsareni daga sharrin Afrah.. Amen ahaka tayi ta juyi asaman gadonta har bacci yayi gaba da ita. 


 Shikuwa yarima yace tashirya sutafi tare na saboda ya batawa Afrah rai don yasan yadda ta tsani Balkisu bazata so tazo gurin ba. Bayan yaga ma abunda yakeyi ne yatashi ya shirya yanufi bangaren mahaifinshi da yake tsammanin yanzu yana chan saboda 5:30 yayi kuma most of d tym irin warhaka yake komawa turakarshi don gana wa da nashi iyalin shima.


  Tafiyake yana danna waya cikin isa da kasaita kamar daga Sama yaji muryar Fahad yana cewa yarima!  Ya tsaya cak batareda yajuyoba, cikin sassarfa yasa meshi yana murmushi yace the CHRMING ya ykk? Sai da yadan ya mutsa fuska yace 😎 cool, yayi murmushi yace da alama dai yau sarautar ta motsa, ya kara daure fuska yace Waya ce maka haka? Sai yayi murmushi yace maida wukar ranka shidade zaka gurin mai martaba ne  ya gyada mishi, yace ok toh muje. 


  Sun yi sa'a kuwa yana bangaren nashi suka shiga suka kwashi gaisuwa mai martaba ya dube su cikin nishadi yace twins din masarauta yau kune atare ya akayi? Fadil yace a'a dama nashigo ne sai yace nan zaizo shine mukazo tare yace masha Allah, Allah yayi muku albarka sukace amen mai martaba ya juya ya kalli yarima yayi murmushi shi kam baisan inda yarima ya gado wannan halin nashi
Na rashin son magana ba, yace yarima akwai maganane yace a'a ba komai daga  nan yayi shiru yaciga ba da danna wayarsa sai Fahad da mai martaba ke fira, sun dan jima kafin yarima ya tashi yayima mai martaba sallama shima Fahad yayi mai sallama suka fita tare. 


 LlllBayan sunfito ne Fahad kedan janshi da fira har yake tambayanshi koyasan batun buffday din Afrah yadan kalleshi yace eh tazo tagayamin dazun yaushe za'ayi i mean wat tym?  Yace Wai 4:00pm saboda atashi da wuri yace ok zan duba nagani da haka dai yagama ya wuce akan cewa sai sun hadu goben. 


Thursday 19/2017

  Yauce ranar da ake yin buffday din Afrah da Farha wanda ita Farhan bataso zuwa ba sai da mum dinsu tasa baki sannan taje. Wow wuri yayi kyau so beautiful anata shagali amma uwar bukin hankalinta yarubu biyu tana tunanin Allah yasa yarima yazo saboda kar abokanta su rainata. A bangaren yarima kuwa naganshi yafito cikin shigar English wears yayi masifar kyau MASHA-ALLAH kai tsaye ya wuce bangaren Umma domin yanason ne ya gani irin shigar da tayi saboda bayaso tayi shigar da bai kamata ba yana shiga ya sameta tayi shiga cikin kanan kaya ta dauko wata abaya mai masifar kyau ta axa Sama ta dauko gyalenta tayi rolling tayi kyau na hakika, yana shigowa ya ganta tsaye zata fito tana sallama da Umma. 


 Suna shigowa gurin hankalin kowa ya dawo kansu ana mamakin kyau irin nasu wasu suna cewa perfect 👌 match Afrah tazo da sauri ta tarbe shi oooh yarima kaxo harna fidda rai tanx bai cemata komai ba saida Farha tazo sannan ta gaida shi ya amsa yadan saki fuska sannan, sai alokacin suka lura da Balkisu da ke gefenshi Farha tace Masha Allah  sisto kinyi kyau Allah Afrah data juya ta juyo arazane tace ke mekike anan waya gayyaceki yarima yace nine idan kuma kinaso zamu iya komawa haryana juya zai fita tashiga gabanshi tace yarima...
Related Posts

Related Posts

Post a Comment