Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana zirga-zirga a cikin garin Jos da kewayen karamar hukumar Jos ta arewa, sakamakon wata ‘yar hatsaniya da ta barke tsakanin matasa da jami’an tsaro, bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara dukkansu ‘yan gida daya a unguwar Rukuba road.
Sakataren riko na gwamnatin jihar Mista Richard Tokma ne ya fitar da sanarwar a maimakon gwamnan jihar, a cewar shi dole a sanya dokar hana zirga-zirgar don dakile fadawa cikin tashin hankali a garin.
‘Mun samu rahoton abinda ya faru jiya, wanda sanadiyyar faruwar shi wasu suke so su kawo tashin-tashina a cikin garin Jos, don haka gwamnan jihar Filato Mista Simon Lalong ya amince da sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe, a kananan hukumomin Jos ta arewa da Jos ta kudu, muna kara kira ga al’umma su kwantar da hankulansu, su kuma kiyayi daukar doka a hannun su.’ inji Mista Tokma.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)