olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 9 A Jos!!


Wasu ‘yan bindiga da ba san ko su waye ba, sun bude wuta a unguwar Rukuba road dake karamar hukumar Jos ta arewa, inda suka sanadiyyar hallaka mutum tara dukkansu ‘yan gida daya.

‘Yan bindigar sun kai haren ne a jiya Alhamis da dare, inda suka bude wuta ba tsayawa na dan wani lokaci, bayan mutum taran da suka rasa ransu, akwai kuma wasu mutanen da suka ji raunuka.

‘Yan bindigar sun yi amfani da lokacin da ruwan saman yake sauka da kuma dare wajen kai harin nasu, duk da akwai jami’an tsaron tabbatar da zaman lafiya na STF, hakan bai hana ‘yan bindigar aikata wannan aikin na ta’addanci ba.

Wadanda suka samu raunuka suna asibitin jan kwano suna karbar magana, sannan jami’an tsaro sun ce zasu zakulo wadanda suka aikata wannan ta’addanci, sannan sun ja kunnen al’umma da su guji daukar doka a hannunsu.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment