Masu ninkaya sun gano gawarwakin mutane 6 daga cikin mutane 9 da Kwalekwale ya kife da su a yankin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere ta Jihar Borno.
Kamfanin dillancin labarai na kasa, (NAN), ya kawo rahoton da ke nu ni da aukuwan hadarin a ranar Juma’a, sa’ilin da mutanan ke tafiya a cikin Kwalekwalen daga Zabarmari zuwa Dusuman.
Mai unguwar na Zabarmari, Bulama Maidamma, wanda ya tabbatar da aukuwan lamarin ya shaida wa manema labarai cewa, mata biyu ne da kuma maza hudu suka mutu a lokacin hadarin, a sa’ailin da aka sami ceto sauran mutanan uku.
Bulama Maidamma ya ce, matan biyu sun shigo Kwalekwalen ne daga Budum, wasun su suna kan hanyar su ne ta zuwa Dusuman domin halartar Sallar Juma’a, sa’ilin da sauran kuma za su tafi halartar Jana’iza ne na wani dan’uwan su.
Ya alakanta hadarin da guguwa mai karfi da ta shafe sama da mintuna 30 tana kadawa a ranar ta Juma’a.
“A tsakiyar rafin ne Kwalekwalen ya jirkice. Yawancin su sai duk suka nutse saboda ba su iya ruwa ba, ba su kuma sanye da rigunan da ke hana nutsewan.
“Mun dai tura masu ninkaya ne domin su lalubo su. Masu ninkayan sun iya ceto uku ne a cikin su har da direban Kwalekwalen a ranar ta Juma’a.
“Neman sauran shidan sai da ya kai mu har ranar Asabar da yamma, kafin mu gano gawarwakin na su.
Malam Muhammed Labo, wanda mazaunin garin na Dusuman ne, ya shaida wa wakilinmu cewa, kanin sa wanda mai gyaran wayoyin hannu ne yana daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, na shiyyar arewa maso gabashin kasar nan, Bashir Garga, ya tabbatar da aukuwan hadarin.
Bashir Garga, ya ce yawancin wadanda hadarin ya rutsa da su suna dawowa ne daga Sallar Juma’ah a ranar ta Juma’a.
Shugaban hukumar ta NEMA a Jihar ta Borno, Malam Bello Danbatta, ya ce an kawo wa hukumar na shi rahoton aukuwar hadarin ne a makare.
Ya kara da cewa, hukumar na shi ta aike da jami’anta wajen domin su gano yanda abin ya faru.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Mista Edet Okon, ya ce har ya zuwa lokacin da wakilinmu ya tuntube shi ba shi da labarin aukuwan hadarin, amma ya ce, zai yi magana bayan ya sami cikakken bayanin yanda abin ya faru.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)