olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Ramos Yana Son Komawa Dan Wasan Tsakiya!



Ga duk mai kallon wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a kwanakwanan nan ya san yadda dan wasan baya na kungiyar, Sergio Ramos yake tafiya ba wai tsakiya ba har ma can gaba inda ya kamata a ce Luka Modric zaa gani a wurin.

Ainihi dai shi dan baya ne mai tare amma yakan tafi cin kwallo a wasu lokutan, wanda hakan ta sanya yake yawan zura kwallaye a ragar a bokan karawarsu musamman a kakar wasnni biyu da suka gabata inda ya zura kwallaye da dama.

To amma sai dai wannan dabi’a tafi yin tsamari tun bayan da sabon mai horas da Madrid Julen Lopetegui ya fara aiki inda yabawa Ramos damar zuwa har kusa da ragar abokan wasa domin cin kwallo.

A wasan da suka buga jiya da Espanyol Ramos ya rinka fita neman cin kwallo ba kakkautawa

duk da neman ci na da amfani amma kuma hakan na iya janyo musu jangwangwama wata rana, yanzu dai an zuba ido ganin ko kocin zai tsawatar masa ko zai kyale shi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni Ramos yafara tunanin komawa dan wasan tsakiya domin cigaba da samun damar zuwa bakin raga domin zura kwallo matakin da ake ganin kamar mai wahala ne.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment