Sabuwar Ministan kudi ta rikon kwarya da aka nada, Uwargida Zainab Ahmed, ta fara aiki awanni 72 da Shugaba Buhari ya nada ta rikon Ma’aikatar kudin, bayan aijiye aikin da tsohuwar Ministar, Kemi Adeosun ta yi a ranar 14 ga watan Satumba.
Kafin dai a nada ta, Zainab Ahmed, ita ce karamar Minista a Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare.
A ranar Juma’a ne Shugaba Buhari ya baiwa Zainab Ahmed, rikon ma’aikatar kudin, bayan da Kemi Adeosun ta yi murabus kasancewan fitowar sakamakon binciken da aka yi kan zargin takardar shaidar tsame ta daga cikin masu yi wa kasa hidima.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)