Rahotannin da suke fitowa daga kamfanin dillancin labaru na Vatican sun ce an yi garkuwa da wani limamin Kirista wanda yake aikin mishan a jamhuriyar Nijar, a yau Talata.
Limamin mai suna Fada Pierluigi Maccalli, wanda yake aiki da wata kungiyar mishan mai suna “Society of African Missions (SMA)”. An sace shi ne da tsakar dare, inji wani Fada mai suna Mauro Armanino wanda suke aiki tare.
Macalli wanda ya shahara da yakar wasu al’adu kamar su kaciyar mata, da sauransu da suka shafi mata, wasu suna ganin dalilin da ya sa aka yi garkuwa da fadan ma Kenan.
Mai magana da yawon gwamnatin Jamhuriyar Nijar, Abdulrahman Zakariya, ya tabbatar da afkuwar lamarin, wanda aka ce ya faro ne a kan iyakar Nijar da kasar Burkina Faso, a yankin Gourmance mai nisan kilomita 125 daga Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Ofishin Jakadancin kasar Italiya a Nijar, ya shawarci hukumomin kasar Nijar da su bi hanya da tafi dacewa wajen ganin an ceto Fadan, wanda ake tunanin masu tsatsauran ra’ayi ne suka yi awon gaba da shi zuwa kasar Burkina Faso inda suke da sansaninsu.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)