olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Yanzu Hankalina Ya Kwanta Tunda Na Fara Cin Kwallo- C.Ronaldo



Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa kawo yanzu hankalinsa ya kwanta tunda ya fara zura kwallo  araga kuma yanzu zai ci gaba da cin kwallaye domin daman aikinsa ne.

Ronaldo dai ya shafe awanni shida bai zura kwallo a raga ba tun  ayan komawarsa kungiyar ta Juventus abinda ake ganin kamar barin Real Madrid ne ya sa hakan ta kasance kuma baya samun ‘yan wasan da zasu dinga taimaka masa.

Ronaldo ya fara zura kwallo a ragar kungiyar Sassulo wanda hakan yasa magoya bayan Juventus suka rude da ihu kafin kuma ya sake jefa kwallo ta biyu wadda itace tabawa Jubentus din damar samun maki uku a wasan.

“Rashin zura kwallo a raga har ya fara damuna saboda duk inda Ka duba idan ana maganar Juventus cewa akeyi har yanzu ban zura kwallo a raga ba hakan yasa na fara tunanin abubuwa da yawa marasa dadi” in ji Ronaldo

Yaci gaba da cewa “kwallon kafa ce daman kuma komai yana ita faruwa a kungiyoyin dana buga a baya ma na taba samun kaina a irin wannan yanayi sai dai surutun bai kai haka ba sai yanzu saboda na bar Real Madrid na koma Juventus”

Juventus dai za ta fara buga wasanta na farko na gasar cin kofin zakarun turai a ranar Laraba inda za ta kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta Balencia dake kasar sipaniya wasan da ake ganin mai wahala ne ga Juventus din wadda take da niyyar lashe gasar ta wannan shekarar.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment