olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

An Sace Motoci 5 Shake Da Mutane A Kaduna!!



A jiya ne wasu barayin mutane suka sace mota biyar shake da mutane a garin Tsuntsaye dake Kauyen Kiriga a Birnin Gwari ta Jihar Kaduna. Inda nan take suka kwashe gabadaya mutane suka yi daji da su.

Bayanin sace mutanen ya fito ne daga bakin Shugaban ‘yan sintirin Birnin Gwari, Ibrahim Nagwari. Wanda ya bada tabbacin cewa an sace mutane da misalin karfe 10:30 na safiyar jiya.

Nagwari ya kara da cewa, maharan sun fara ne da sace wani direban mota kirar ‘Bolkswagen Golf’ tare kuma da sace dukkan mutanen da suke cikin wasu motoci guda hudu.

“Wannan lamarin ya afku ne kasa da awa goma da wani danmu mai mukamin kaftin ya damke wani sojan bogi.

“Muna kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta baci a wannan yanki na Birnin Gwari har sai an tarwatsa gungun wadannan barayin shanun.

“A lokaci guda kuma muna kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu. Kuma mun ba rundunar soji awa 48 da ta yi wa jama’a bayani dangane da wannan sojan bogi da kuma masu hannu cikin wannan ta’asa, ba tare da la’akari da girmansu a wannan yankin ba.

“Haka kuma muna kira ga gwamnatin Jihar Kaduna da ta nunawa duniya cewa ta damu da halin da al’ummar wannan yanki suke ciki, ta hanyar fitar da ko da kasidar manema labarai ne, wanda suka gaza cewa komi tun bayan da aka yiwa sama da mutum 76 kisan gilla a garin Gwaska.” inji shi

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce tuni an tura rundunar ‘yan sanda don su yi bincike a yankin.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment