Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana siyasar kudi a matsayin babban abin da ke janyo lalacewar gwamnati a kasar nan.
Basaraken na Sakkwato, wanda kuma shi ne babban shugaban majalisar koli ta harkokin Addinin Musulunci, ya yi wannan maganan ne a wajen wani taro na 23 na al’ummar Musulmi wanda kungiyar, ‘Ummah Mobement, ta shirya a Abuja.
Taken taron shi ne, ‘Muryan Musulmi a Kan Shugabanci nagari a Nijeriya.’
Ya kuma yi jimamin yanda siyasar kasar nan ta lalace, take kuma ci gaba da tabarbarewa a kullum, ta yanda kudi suka zama su ne komai, “Ba ta yanda za mu bari kudi su zama su ne komai sannan mu yi tunanin kawar da cin hanci da rashawa.
“Wannan kuma shi ne musabbabin rashin samun shugabanci nagari wanda ya dabaibaye mu, yake kuma dankwafar da ci gaban mu, yake kara jefa mana talauci da rigingimun da suka ki ci, suka ki cinyewa.
“Irin wannan siyasar ta kudi za ta ci gaba ne da habaka cin hanci da rashawa a cikin al’ummarmu, wanda a sakamakon hakan, yana nu na irin hadarin da zuriyar mu ne ke cikin sa.
“Ya zama tilas ga dukkanin shugabanni, shugabannin Addini da Sarakunan gargajiya da su hada kai domin ceto tsarin namu na siyasa da ke tafiya a kasar nan.
“Mummunan sakamakon yin ko in kula, da abin da ke faruwan, ya nu na ya fa zama tilas da mu mike tsaye mu yi wani abu kafin wuri ya kure,” in ji Sultan.
Ya shawarci shugabanni a dukkanin matakai da su dauki lamarin shugabanci da mahimmanci, yana mai cewa, “Ba zai yiwu mu manta da yanda tarihi ya dora mahimmanci a kan shugabancin ba.”
Ya ce, a Musulunci, shugabanci kowane iri abu ne mai matukar mahimmanci, wanda amana ne daga Allah, wanda kuma za a tambayi duk wadanda aka baiwa amanan su yi bayani a kansa.
Basaraken ya shawarci Musulmi da su kasance a sahun gaba wajen nu na kyakkyawan shugabanci abin koyi.
Sultan ya yi nu ni da cewa, shugabancin hakki ne na al’umma, wanda aka shirya shi domin kula da jin dadi da tsaro ga dukkanin ‘yan kasa, wanda ya kwatanta matsayin masu mulki daidai da na wadanda ake mulka.
Tun da farko, Uwargida Amina Omoti, tsohuwar Shugabar kungiyar ta tarayyan mata Musulmi ta kasar nan, (FOMWAN), cewa ta yi, kyakkyawan shugabancin yana da mahimmanci a kowane abu na rayuwar dan adam.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)