Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ba za ta iya fitar da kudin da Manchester United zata bukata ba wajen siyan dan wasa Paul Pogba wanda suke rikici da kociyan kungiyar Jose Mourinho.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da PSG da Jubentus ne dai aka bayyana suna zawarcin dan wasan dan asalin kasar Faransa wanda yakoma Manchester United daga kungiyar kwallon kafa ta Jubentus.
Sai dai mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Enesto Balberde yaki cewa komai bayan da aka tambayeshi ko kungiyar zata nemi dan wasan a watan Janairu mai kamawa idan an bude kasuwar siyan ‘yan wasa.
Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa Barcelona bata da kudin da zata iya siyan dan wasan da kuma albashin da zata dinga biyansa bayan da aka bayyana cewa tuni kungiyar ta ware kudi fam miliyan 564 wanda zata biya ‘yan wasanta albashin wannan kakar.
Idan har kungiyar zata siyeshi a wannan lokacin zata kashe kudi fam miliyan 150 har da albashinsa da zata dinga bashi har zuwa karshen kakar wasa kuma hakan zai kawo nakasu ga tafiyar da kungiyar.
Sai dai idan har Barcelona tanason siyan Pogba sai dai ta siyar da daya daga cikin manyan ‘yan wasan da suke kungiyar a yanzu, hakan kuma ya dogara ne kacokan ga irin soyayyar da shugaban kungiyar yakewa dan wasan.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)