Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Kylor Nabas ya bayyana cewa rashin dan wasa mai zura kwallo a raga kamar Cristiano Ronaldo har yanzu shine matsalar kungiyar kuma yakamata a dauki mataki akai.
Real Madrid tayi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow a wasa na biyu na gasar cin kofin zakarun turai da kungiyoyin suka fafata a ranar Talata a kasar Rasha.
Wannan dai shine wasa na hudu da Real Madrid ta buga a gasar laliga data zakarun turai batare data samu nasara ba kuma hakan yakawo ayar tambaya akan kociyan kungiyar Julian Lepatugui.
“Ronaldo yabar gubi sosai a Real madrid kuma har yanzu bamu magance matsalar daya bari ba kuma babu alamar yin hakan saboda haka yakamata hukumomi su dauki mataki akai kafin abubuwa suci gaba dayinrashin dadi” in ji mai tsaron ragar.
Yaci gaba da cewa” bazaka rufe rana da tafin hannu ba saboda Ronaldo ya zura kwallaye a raga lokacin da yake tare damu sai dai dole mu manta dashi tunda yanzu baya tare damu kuma mu fuskanci abinda yake gabanmu”
Real Madrid dai ta siyar da Ronaldo ga kungiyar kwallon kafa ta Jubentus din kasar Italia akan kudi fam miliyan 105 sai dai kuma har yanzu kungiyar bata siyo wanda zai maye mata gurbinsa ba.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)