olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Shin Da Gaske Ne Yanzu An Daina Tsoron Madrid?!



Real Madrid mai rike da kambin gasar cin kofin zakarun Turai ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a hannun CSKA Moscow a Rasha, kuma a karon farko kenan da Madrid ke buga wasanni uku a jere ba tare da jefa kwallo ko guda ba tun shekarar 2007, zamanin Fabio Capello.

Nikolas Blasic ne ya zura kwallon daya tilo a ragar Madrid kuma dama ya koma CSKA Moscow ne akan aro daga Eberton bayan ya buga wasannin firimiyar Ingila har sau 12 ba tare da jefa kwallo ko guda ba.

Karim Benzema da Casemiro da Mariano duk sun yi bakin kokarinsu na ganin sun farke wa Madrid kwallon da aka zura mata amma abin ya gagara bayan da suka daki turken raga kowannensu.

Sergio Ramos an hutar da shi daga buga wasan na ranar Talata, yayin da Luca Modrid da ya lashe kyuatar gwarzon dan kwallon duniya ke cikin wadanda aka fara ajiyewa a banci.

Gareth Bale bai buga wasan ba saboda raunin da yake fama da shi inda a karon farko kenan da CSKA Moscow ke samun nasara a dukkanin haduwa uku ta yi da Real Madrid a gasar zakarun Turai.

Sai dai wasu suna ganin kungiyar yanzu ba’a jin tsoronta kamar kakar wasan data gabata saboda babu wani babban dan wasa kamar Ronaldo.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment