olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Inso Nafi Messi Kafa Tarihi A Duniya!!



Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harry Kane, ya ce yana so ya wuce bajintar cin kwallayen dan wasan Barcelona Lionel Messi domin shima yakafa babban tarihia  duniya.

Kane, mai shekaru 25 a duniya, kungiyarsa ta fafata ne da Barcelona a ranar Laraba a gida a wasan rukunin B na Gasar Zakarun Turai.

“Messi yana shigewa gaba wajen nuna bajinta hakan kuma yana ba ni kwarin gwiwar kara zage damtse domin nima naga ana maganata a duniya kamar yadda kullum ake maganarsa,” in ji Kane.

Yaci gaba da cewa “Ina fatan wata rana zan ci kwallaye da yawa, idan ban ma wuce dan wasan ba ke nan kuma tabbas idan naci gaba da dagewa ina kuma samun taimako zanyi abinda yafi haka.”

Dan kwallon Ingilan shi ne ya fi kowa zura kwallaye a raga a kakar wasanni ukun gasar firimiya da suka gabata kuma shi ne wanda ya fi cin kwallaye a Gasar Cin Kofin Duniya wadda aka yi bana a kasar Rasha.

A karshen makon jiya ne adadin kwallayen da dan wasan ya zura a raga suka kai 145 a lokacin wasansu da kungiyar Huddersfield a gasar firimiyar kasar Ingila.

Sai dai Kane yana bayan Messi wanda ya zura kwallaye 560 a raga, kuma ya zura guda 103 ne a Gasar Zakarun Turai.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment