Kungiyar Boko Haram bangaran Mamman Nur ta kashe kwamandanta mai suna Ali Garga bisa laifin cin amanar kunguyar.
Majiyarmu ta bayyana mana cewa kafin asirinsa ya tonu dai, Garga yana shirin sakin matane 300 wadanda kungiyar ta kama. Sun dai samu nasarar cefke shi, inda wani kwamanda daga cikin ‘ya’yan kungiyar bangaran Mamman Nur ya kashe shi. majiyar tamu ta kara tabbatar da cewa Garga yana sirin mika kansa ga rundunar sojan Nijeriya. An dai kashe Garga ranar Alhamis lokacin da yake kokarin aiwatar da shirin nasa. Shi dai Garga bafulatani ne daga jihar Taraba, ya dai shiga wannan kungiya ne shekaru uku baya lokacin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kame masa shanunsa a yankin Chadi. Majiyarmu ta kara da cewa “kungiyar ce ta koya ma Garga yadda ake kai hare-hare.
“Ya dai yi saurin iya yadda ake kai harin ne saboda shi bafulatani ne. Wannan shi ya sa har ya kai matsayin kwamanda a cikin kungiyar Boko Haran bangaran Mamman Nur.
“Garga ba ya sha’awar yadda ake kama mutane domin a biya kudin fansa. Abin da yake sha’awa shi ne dabbobinsa su dawo gare shi sannan ya ci gaba da kiwansa kamar yadda yake dun da.”
Kafin a kashe Garga, ya shirya yarjejeniya shi da wadansu ‘yan kasan waje, ta hanyar da za su bi domin su kubutar da shi da kuma sauran wadanda suka kama.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)