olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Har Yanzu Bamu Shiga Damuwa Ba - Leonel Messi!!



Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, ya bayyana cewa kungiyar tasa bata cikin wani hali duk da cewa ta yi wasa uku batare data samu nasara ba a gasar laliga ta wannan shekarar da ake fafatawa.

Barcelona dai ta shiga filin wasa domin fafata wasa da kungiyar Athletico Bilbao bayan da kungiyar takasa samun nasara a wasanni biyu na baya data buga da kungiyoyin Legannes da Girona.

Dan wasa Oscar Di Marcos ne ya zurawa kungiyar Athletico Bilbao kwallonta ta farko a raga sai dai dab da za’a tashi daga wasan dan wasa Haddadi ya farkewa Barcelona kwallonta kuma aka tashi wasa 1-1 a filin wasa na Nou Camp

Sai dai tun da farko Barcelona tafara wasanne batare da dan wasa Messi ba bayan da kociyan kungiyar ya ajiye dan wasan domin ya huta sakamakon kungiyar zata buga wasa da kuyngiyar Tottenham a gasar cin kofin zakarun turai a ranar Laraba.

“Tabbas sakamakon da muka samu a wasan mu da Bilbao bah aka mukaso ba amma kuma babu yadda zamuyi saboda yanayin wasa ne komai yana iya faruwa sai dai duk da haka bamu shiga cikin wani hali na dimuwa ba” in ji Messi

Yaci gaba da cewa “Muna fatan nan gaba a wasan da zamu buga a gaba mu samu nasara saboda ansan Barcelona da samun nasara a wasanni kuma daman babu wanda yasan abinda zai faru a wasa sai idan antashi.

Shima kociyan kungiyar yayi kira ga ‘yan wasan kungiyar dasu ci gaba da dagewa domin kakar wasan wannan  shekarar tazo da abin mamaki kuma idan basuyi da gaske ba za su sha wahala sosai.

Related Posts

Related Posts

Post a Comment