Sunan CR7 na daga cikin manyan sunan inkiyar da ake jin duriyarsu a duniyar kwallon kafa a wannan lokacin amma kuma sai dai ba kowa ne ya san wasu bayanai game da shi ba.
Da farko dai ya kamata kusan cewa sunan CR7 suna ne da aka zakulo shi daga sunayen shahararren dan kwallon nan wato Cristiano Ronaldo da kuma riga mai lamba 7 da ya goya a tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United da Real Madrid da kuma yanzu a Juventus.
Kamfanin dayake yin kayan wasanni na (Nike) kuma wanda yake daukar nauyin kera takalman da yake sanyawa a shekarun baya sun buga takalman dan wasan kasar Brazil babban Ronaldo mai dauke da tambarin inkiyar ‘R9’ wanda ya kuma karbu sosai tun a shekarar 1998.
Ganin nasarar da suka yi a kan wancan ne ya sanya suka sake yiwa Ronaldo karami nasa kalar CR7 kuma shima kamar yadda abubuwa suka nuna tabbas sunyi nasara akan hakan.
To amma sai dai dan wasan ya cigaba da bunkasa kansa ta hanyar bude nasa kasuwancin mai dauke da inkiyar CR7 a kasashe irinsu China da kasarsa ta haihuwa Portugal da kuma wanda za’a bude nan gaba kadan a Paris, babban birnin kasar Faransa.
Ya bude kamfanin turare mai sunan “CR7 sannan kuma ya bude kamfanin siyar da kayan sawa ‘yan ciki mai suna “CR7 Underwear” wanda yanzu haka ya samu karbuwa sosai a kasashen duniya musamman Amurka.
A shekarar 2013 ne kuma aka bude wani gidan tarihi a kasarsu wanda ake kiransa da Museu CR7 Baya ga haka, Dan wasan yayi haDin gwiwa da wasu manyan kamfanoni suka tsunduma harkar masaukin baki (Hotel) har aka sanyawa hotel Din sunan CR7 Hotels yanzu kuma yana shirin bude wasun Otal din a garuruwan New York na Amurka da birnin Madrid da kuma birnin Marrakech na kasar Morocco.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)