olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

HausaNovel: Dan Sarki Book 1 Chapter [5]



 Dan sarki chapter 5
             
 Tasha gabanshi tace yarima don Allah katsaya ni bansan tare kuke ba kayi hakuri, ya kalleta ya kawar da kai yace ita zakiba hakuri ai bani ba ta zaro ido👀 tace ita kuma yace yes and if u can't ki bamu hanya mu wuce i have better things to do ta juya ta kalli mutanen da ke gurin taga hankalinsu be gurin sannan tajuyo ta kalli Balkisu dake tsaye ta sadda kanta kasa tace kiyi hakuri tanayi tana hararar ta, tace aiba komai ya wuce sai alokacin yarima ya juya zai shiga ciki tace yauwa yarima pls zaku dan gaisa da friends dina ya kalleta a wulakance yace ur welcome harta juya yace a gurin buffday din muba muda seat 💺 ne tajuyo tace sorry i was carried away kai ka zauna akan high table ita kuma she can seat any where, ya kalleta yace no don't worry zamu zauna anywhere din tare tace no ai kai dan seat dinka ne mana high table yace if so sai muzauna tare a high table din, bata da zabi face tayarda.



Kai Afrah wace waccen tareda yariman ki? (Wata kawartace ke tambayarta), saida ta yamutsa fuska tace wai secretary din maman shi ce, suka juya suka kare Mata kallo wata kuma tace amma kam sai kin tashi tsaye wannan kyaun, Afrah tayi tsaki mtswwww amma dai ke banza ce wannan ne kyau unmm bama shiba yanzu dai muje ku gaisa.


A high table na gansu kowace sai kwarkwasa takeyi sofie ce ta fara magana tace hi 👋 am Safiya Alhasan Naira by name nice meeting u, bai ko kalleta ba itama Hauwaty ta hau nata kwarkwasa am Hauwa'u Ibrahim sai Balkisu ce tace ur welcome. Haka suka juya gwiwa a sace suna masu jin haushin abunda yarima yayi musu.



30 mins latter



An yanka cake 🍰 inda Afrah ta bukaci yarima da  yazo suyi tare amma yace shi ya wakilta Balkisu su yanka tare Afrah taji haushi matuka amma yaza tayi tunda hausawa sunce abunda kakeso ke wahalar dakai bayan sun gama yanka cake yarima ya mike yace shi zai wuce Farha ce ta rakasu har gurin motarsu sannan suka wuce.



Ba gida suka nufa ba wata   unguwa suka nufa wurin quiet ne bakajin motsin komai sai kukan tsuntsayen gidajen gurin wani gida suka nufa inda kafin sukai gate din yabude da kanshi suka shiga ciki Balkisu ce ta fito tayi tsaye tana jiran yagama mulkin nashi ya fito. Kofar motar ya bude yafito sannan yayi gaba yabarta tsaye dole tabi bayanshi tana tunani to meya kawosu nan ne............. (Nina dai sai nace bansaniba...
Related Posts

Related Posts

Post a Comment