olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Hukumar Kwallon Kafar Turai Zata Hukunta Manchester United!!



Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, ta kaddamar da bincike domin daukar matakin ladabatar da kungiyar Manchester United, sakamakon rashin mutunta lokaci da kungiyar ta yi, a wasan gasar zakarun turai da ta fafata da Balencia a ranar Laraba.

‘Yan wasan kungiyar ta Manchester United da suka karbi bakuncin Balencia, sun gaza isowa filinsu na Old Trafford akan lokaci, lamarin da ya tilasta, rashin soma wasan na jiya da aka tashi babu ci 0-0, da lattin mintuna biyar.

Hukumar UEFA ta ce sai a ranar 18 ga watan da muke ciki, za ta sanar da hukuncin da za ta yanke kan kungiyar ta Manchester United domin gujewa faruwar hakan anan gaba.

Kafin wannan lokacin dai, mai horar da ‘yan wasan kungiyar, Jose Mourinho, ya ce rashin baiwa tawagar ‘yan wasansa rakiyar jami’an ‘yan sanda zuwa filin wasansu kamar yadda aka saba ne ya jawo musu bata lokacin da basu saba ba, inda suka shafe mintuna 45 daga Otal dinsu zuwa fili.

To sai dai rundunar ‘yan sandan birnin Manchester, ta ce ba tada laifi ko kadan, don kuwa ta sanar da kungiyar sauyin da aka samu, akan dokar basu rakiya daga masaukinsu zuwa filin wasa, a duk lokacin da zasu fafata, wadda aka janye ta.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment