olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Ronaldo Ya Mayar Da Martani Bisa Zargin Yin Fyade!!


Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo ya yi watsi da zargin cewa ya yi wa wata mata fyade a wani otel a Amurka kimanin shekara goma da suka gabata.

Tsohon dan wasan gaban Real Madrid din, mai shekara 33, ya ce hankalinsa a kwance yake kan duk wani bincike da za a gudanar a kansa kan zargin cewa ya far wa Kathryn Mayorga a wani daki a otel din Las Begas a shekarar 2009.

Ronaldo ya yi maganar ne gabanin lauyoyinta su gabatar da wani taron manema labarai a ranar Laraba inda suke zargin tsohon dan wasan Manchester United din dayin aika aikar da suke zarginsa dayi.

A can baya dai ya ce zargin, wanda wata mujalla ta kasar Jamus Der Spiegel ta fara wallafawa labarin “kanzon kurege ne kuma bai kamata mutane su yarda da abinda mujallar ta buga ba.”

Mujallar Der Spiegel ta ce Mayorga, mai shekara 34, ta shigar da korafi ga ofishin ‘yan sanda na Las Begas jim kadan bayan da lamarin da take zargin ya faru.

Amma shakara guda bayan wannan, an ruwaito cewa sun sasanta ita da Ronaldon ba tare da sa bakin kotu ba, inda ya ba ta dala 375,000 da yarjejeniyar cewa ba za ta fallasa batun ba.

A yanzu haka lauyoyinta suna so su wargaza waccar yarjejeniyar ta farko sai dai a ranar Talata ‘yan sandan birnin Las Vegas sun tabbatar da cewa a baya sun yi bincike kan korafin a watan Yunin 2009, amma sun kara da cewa babu wanda suke zargi a lamarin.

Wata sanarwa ta ce: “Duk lokacin da aka dauka na shigar da korafin, matar ba ta sanar da ‘yan sanda wajen da abin ya faru ba kuma a watan Satumbar 2018 ne aka sake waiwayar shari’ar kuma jami’an ‘yan sanda suna bin diddigin bayanan da aka samar.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment