Kanawa kan ce “Kano Timbin giwa, yaro ko da me ka zo an fika”. Hakika a shekarun baya wannan Magana haka ta ke babu ja, amma da wahala a yanzu mutane su yarda da wannan ikirari.
Kano ta kasance zakaran gwajin dafi tsawon daruruwan shekaru, kama daga shekara ta 999 bayan zuwan Annabi Isa sanda aka kafa daular Habe har zuwa tsakiyar karni na ashirin. Turawan mulki mallaka ba su hakikance da mamaye Nigeria ba, duk da cewa sun kama garin Sakkwato, sai da sojojin Kanar Thomas Moorland su ka murkushe sojojin Kano a yaki cikin shekarar 1903.
Duk da mamayar ‘yan mulkin mallaka, matsayin garin Kano na ja-gaba cikin garuruwan Hausa da ma kasar Nigeria bai canza ba, sai dai ma habaka da ya kara yi sakamakon zuwan turawa ya habaka harkar noma wadda Kanawa su ka shahara a kai. Samar da layin dogo cikin shekarar 1912 ya sa Kano ta zama tashar jirgin kasa mafi mahimmanci a kasar Nigeria, a matsayinta na madakatar jirgi da kuma zama cibiyar rarrabawa da daukar kaya a duk fadin arewacin Nigeria da Nijar. A shekarar 1935 an gina filin jirgin sama na farko a birnin Kano, wanda ya fara jigila duk sati zuwa birnin Khartoum na Sudan a kan hanyar jirage da ke tasowa daga London zuwa kano su wuce kasar Afirka ta kudu. A lokacin yakin duniya na biyu kuma sai tashar filin jirgin ta zama wata cibiya wadda Amurka ke amfani da ita domin isa kasashen gabas ta tsakiya da gabas mai nisa. Bayan yakin duniya na biyu Kano ta kasance gari mafi zama irin na zamani a arewacin Nigeria tare da kasancewa inda aka fi ko’ina noman gyada. Kano ke samar da kusan rabin ilahirin gyadar da Nigeria ke samawar a wannan lokaci, abinda ya bai wa Nigeria matsayin kasar da ta fi kowacce a duniya yawan samar da gyada kuma hanya mafi girma wajen samarwa da kasar kudaden shigarta.
Daya daga cikin sirrin wannan nasara ta Kano shine samun shugabanci na-gari wanda marigayi Abdullahi Bayero tare da sauran manya a garin ke bayarwa karkashin masarauta da hukumar N.A. Tun a shekarun 1949 shugabannin Kano sun samar da tsarin tattalin arziki da ci-gaba na shekaru biyar wanda daga baya a ka maida shi na shekaru goma. An assasa noman gyada ta hanyar bada tallafi ga manoma tun cikin kaka domin su shiryawa damuna a karkashin dillalan siyen gyada a hannun manoma (Lisensed Buying Agents) tare da kafa hukumar cinikayyar noma (Marketing Board) wadda a ka kirkira a shekarar 1950. Da farko kwarori, wadanda su ka shigo birnin Kano tun a shekarun 1930, sun mamaye wannan dillanci amma sai shugabanni su ka assasa dillalai ‘yan kasa irin su Alhassan Dantata wanda ya zama cikin mafiya arziki a yammacin Afirka. Lokacin Abdullahi Bayero an assasa harkar ilimin boko yadda da karfin tsiya aka rika kwatar yara ana kaisu makaranta saboda hangen nesansa, kuma aka rika rubuce-rubuce da fassara littafai. Bayan yakin duniya na biyu akwai kimanin madabba’ar buga littafai na ma su zaman kansu guda shida banda na hukumar N.A.
Abin takaici, al’amuran Kano sun fara samun koma-baya a karshen shekarun 1950 lokacin da aka nada sarkin Kano Muhammadu Sunusi, kuma har yanzu wannan koma baya na tafiya. Ina dalili? Dalili shine maimakon shugabanni da hukumomi su gina a kan tsarin Abdullahi Bayero sai su ka yi sakaci tare da maida hankali ga la’amuran addini, na mulki da gina kai. A wannan lokaci sarkin Kano na daukar albashi na fam dubu takwas, wazirinsa na daukar fam dubu da dari biyar amma karamin ma’aikacin N.A. bai wuce fam dari ba. Sarkin Kano ya shekara goma a jere, wato iya tsawon mulkinsa yadda a duk shekara sai ya je aikin hajji sannan ga bada kyauta ta ban mamaki ga malaman addini. Na tuna wata hira da Dan Masanin Kano ya yi, inda ya ke yabon Sarki Sunusi kuma a kaikaice ya ke rage kimar Audu Bako domin ya na cewa duk ayyukan da Audu Bakon ya yi, Sunusi ne ya fara kirkiro su, domin akwai wani abokinsa baturen ingila da suka hadu da Sarki a can Ingila, ya nemi ya zo Kano domin ya bada shawara kan harkar noma. Da Baturen ya zo ya yi yawo da bincike da nazari inda ya fitar da wani tsari da za’a amfani kogunan Kano ta hanyar yin madatsun ruwa da za su bada damar noma duk tsawon shekara. Sarki ya bawa ma’aikatan N.A. su duba tsarin su bada shawara. Bayan sun duba sai su ka ce aikin ya fi karfin N.A. sai dai ko gwamnatin Arewa. Shi wannan Bature ya nemi a tura shi ya je ya yi wa Sardauna bayani, ya je amma dai a karshe ba’a aiwatar da tsarin ba sai bayan shekaru kusan goma da Audu Bako ya zama gwamna na farko a Kano, inda ya dauki wannan tsari ya fara aiwatar da shi. Duk da cewa kaso kalilan ya aiwatar, amma tasirin ayyukansa na nan har yanzu kuma zasu ci gaba da tasiri shekaru masu zuwa nan gaba. Domin daya daga cikin Dam din da ya yi shine na Tiga, wanda miliyoyin mutane ke amfana a tsakanin kananan hukumomi kusan biyar
Marigayi Malam Aminu Kano ya aiwatar da tsarin jam’iyyarsa ta PRP karkashin mulkin Abubakar Rimi abinda ya kawo gagarumin ci gaba ta kowacce fuska a cigaban jihar Kano. Amma duk da irin aikin da Abubakar Rimi ya yi, an kada shi a zaben gwamna na shekarar 1983, ba don komai ba sai don kaucewa tsarin jam’iyyar PRP. Wannan ne ya kawo ni kan makasudin wannan rubutu nawa na yau, wato abubuwan da mu ke gani na faruwa a jihar Lagos game da zaben fitar da dan takara, abinda ya jaddada irin wancan abu da ya faru a Kano karkashin Malam Aminu Kano a zaben 1983. Tinubu ya tsaya kai da fata cewa lallai sai an kawar da Gwamna Ambode, duk da cewa daga shekarar 2015 zuwa yanzu babu wani gwamna a Nigeria da ya yi rabin-rabin aikin da ya yi. Dalili kuwa shine tun zuwan Tinubu a 1999, masu ruwa da tsaki na jihar Lagos sun fitar da tsarin ci gaban tattalin arzikin jihar na shekaru 25 (abinda Kano ta fara shekaru 70 da suka gabata) wanda Tinubu ya bi tsawon shekaru 8, ya bawa Fashola wanda shi ma ya bi tsawon shekaru 8. Amma Ambode ya kaucewa wannan tsarin don haka dole su Tinubu su kawar dashi domin ba mutum ake yi ba sai abinda zai amfani al’umma. Wannan shine tsari na siyasa mai inganci wanda muka rasa a yanzu a Kano, duk da cewa Aminu Kano ne ya fara aiwatar da shi a nan. Abin takaici, tsawon shekaru takwas na Kwankwaso da ya yi, tare da shekaru takwas na Shekarau da alamu kuma wasu takwas din da Ganduje zai iya yi, idan ba wani kadaru na Allah ba, sun kasance tsawon rubu’in Karni guda da aka banzatar ba tare da samun wani gagarumin canji a Kano ba sai yaudara, sacewa da barnatar da kudaden jihar. Ganduje ya makale wa Buhari ya ci zabe kuma ya na neman sake makela masa don komawa. Saboda tsagwaron munafinci, Ganduje ya ce zai yi zaben kato-bayan-kato amma sai ga shi an maida zaben na nune da dora mutane wadanda ke adawa da al’umma domin ba sa kishinsu ba sa kishin Buhari. Ka dauki mazabar sanata ta Kano ta tsakiya wadda tun daga 1999 lokacin Kura Muhammed har zuwa lokacin Kwankwaso a 2015, ba’a taba samun sanatan da ya yi aiki da tallafawa al’umma kamar Lado ba. Lado ya bar PDP ya dawo APC domin ya sake takarar sanata, ya yi kamfe lungu lungu amma da rana tsaka sai ga Ganduje ya lalubo Shekarau ya sa shi tsayawa takarar kujerar. Shi kuma Lado don sakarci maimakon ya jajirce ya tsaya koda za’a kada shi kamar yadda Kwankwaso ya danne shi a 2015, ko don masu goyon bayansa, sai ya bada kai bori ya hau. Me Shekarau zai tsinana mana a Kano ta tsakiya idan banda ya je majalisa ya zama wani Bukola Sarakin? Domin duk da cewa Allah ne ya daukaka shi, amma ta silar Buhari ne, kuma bai taba boye kiyayyarsa ga irin tsarin da Buhari ya yarda da shi ba na kulawa da hakkokin talakawa.
Sannan a Kano ta Arewa, tsohon mataimakin gwamna shi ma don sakarci aka sa shi ya janye wa sanata mai ci. Ta yaya talaka zai yarda da cewa dama takarar don shi ake yi ba don biyan bukatar kashin kai ba ce? A mazabar sanata ta kudu kuwa saboda dan gani kashenin Buhari ne ya tsaya, wanda sun san cewa ba za su iya tilasta shi ya janye ba sai aka yi abinda aka yi wajen kada shi da tabbatar da sanatan da ya ke kai wanda shi ma bai taba boye cewar shi yaron Saraki ba ne.
Akwai wani abokina na kusa wanda ya ce min zai tsaya takarar dan majalisa amma sai na bashi shawarar kada ya tsaya domin a ganina ofishin da ya ke jagoranta ya fi na sanata amfani. Shugaban wata hukumar gwamnatin tarayya ce, da hadin gwiwar kungiyar lafiya ta duniya (WHO) kuma kasashe 41 ke karkashin hukumar tasa. A shekara daya da zama shugaban wannan hukuma ya bawa mutane 50 aiki, sannan kuma an sahale masa daukar karin wasu mutane 200. Akwai sanatan da zai iya samar da wadannan guraben aiki ga mutane tsawon shekara 8? A lokacin da gwamna ya kira su taron sasantawa, sai dai kawai ya kallin wannan ya ce ka janye wa wancan. Shi kuwa abokin nawa ko sunansa gwamnan bai kira ba a jerin yan takarkaru shida daga mazabarsa, watakila ko don shi kadai ne kwararren Likita a cikin ‘yan takarar?
Mu sani matukar ba za mu iya zaben wadanda muke so kuma wadanda su ka cancanta ba, wallahi haka zamu yi ta zama bayin yan siyasa. Buhari kadai ke son talaka a kasar nan kuma ba shi da mataimaka, amma duk da haka dai kasar na motsawa gaba sannu-a-hankali. Don haka wajibi mu jajirce ganin cewa ba mu zura ido ana mana kama karya ba. Yaki ne dole mu yi shi duk da cewa ba za mu iya canza baya, ba amma dai muna iya amfani da yanzu wajen ganin mun kyautata gobenmu.abubakarsadi.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)