Tuni dai labarai suka bayyana rashin jituwa tsakanin dan wasa Paul Pogba da kuma kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho inda har takai suna fadar bakaken maganganu a filin daukar horo.
Neymar da Pogba dai abokan juna ne tun lokacin da dan wasan yana Barcelona kuma dan wasan tun a lokutan baya yaso yaja hankalin Pogba daya koma Barcelona da buga wasa kafin shima yabar Barcelona
Sai dai kungiyar kwallon kafa ta PSG a halin yanzu bata da kudin da zata iya siyan Pogba duk da irin kasafin kudin kungiyar amma dokar hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai tasa dole kungiyar bazata kashe kudi sama da yadda doka ta tsara ba.
Dan wasa Neymar yana ganin komawar Pogba kungiyar zai taimakawa kungiyar wajen sake cike gurbin da yake tsakaninta da Barcelona da Real Madrid da kuma Jubentus sai dai abune mai wahala cinikin ya kasance a watan Janairu.
Shi ma Neymar a kwanakin baya an danganta shi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sai dai daga baya kuma ya hakura yaci gaba da zama a PSG saboda a cewarsa kungiyar tanada shiri mai kyau.
Kungiyar PSG dai kawo yanzu tanada manyan ‘yan wasan da suka hada da Neymar din da Kylian Mbappe da Angel Di Maria da mai tsaron raga Buffon wanda yakoma kungiyar a wannan kakar.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)