olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Nigeria Na Iya Zama Cibiyar Talauci Ta Duniya- Sarkin Kano!!


Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi Lamido Sanusi II, ya yi gargadin cewa Nijeriya za ta iya kasancewa cibiyar talauci ta duniya nan da shekaru 30 masu zuwa, a sakamakon yin amfani da tsaffin dokoki da tsare-tsare.

Yana mai cewa, ya zama tilas gwamnati ta dauki matakin hana aukuwan wannan annoban.

Sarkin ya yi wannan gargadin ne a sa’ilin da yake jawabin karban mukamin girmamawan da aka ba shi na matsayin wakili a Klub din, ‘Sigma Club,’ na Jami’ar Ibadan, wanda aka yi a harabar Jami’ar a karshen makon nan.

Sarkin wanda ya bayyana cewa, ya ziyarci kasar Amurka a kwanan nan domin halartar babban taron majalisar Dinkin Duniya, ya ce daya daga cikin zaman da ya yi bakin cikin rashin samun halarta shi ne, zaman da aka yi da hamshakin attajirin nan na duniya, Bill Gate, inda attajirin ya yi magana a kan yanda talauci ke mamaye duniya da kuma ci bayan da talaucin ke yi a duniyar. A cewar shi, Bill Gate, ya janyo hankalin duniya ne da cewa, a lokuta da yawa, “in muka yi la’akari da manyan lambobi ba tare da mun fassara su ba, mukan rasa gane mahimman abubuwa.

“A kan yadda lissafin yake, in har a ce kowace kasa za ta ci gaba da tafiya a kan tsarin da take a halin yanzun, to daga nan zuwa shekarar 2050, kashi 80 na matalautan duniya za su kasance ne a nahiyar Afrika. To ba ma a nan ne firgicin yake ba. Rabin wannan kashi 80 din, za su kasance ne a Nijeriya da kuma kasar Jamhuriyan Congo. Kasashen biyu su ne za su kasance da kashi 40 na matalautan duniya, wannan kuma shi ne zai sabbaba kasancewar Nijeriya a matsayin shalkwatar matalautan duniya baki daya.”

Sarki Sanusi, wanda tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya ne ya ce, “Wannan fa kasa ce wacce ta haifar da manyan mutane masu yawa. Wannan fa kasa ce da take yin alfahari da haifar da Farfesoshi da manyan masana tuli tari. Me ya sanya kasashen Sin, Taiwan, Singafore, Hong Kong, Koriya ta kudu, da sauran su masu yawa. Mutane sun manta da cewa, a shekarar 1960, hukumar bayar da shawara ta kasar Amurka takan baiwa mutananta shawarar su zo Nijeriya ne su zuba jarin su ba Japan ba, domin a wancan zamanin Nijeriya ce ke da kyakkyawan mahanga.

“A shekarar 1960, kudin shigan da Nijeriya ke samu ya zarta na kasashen Koriya ta kudu da kasar Sin. Mahaifina shi ne Jakadan Nijeriya na farko a kasar Sin, a shekarar 1972. A shekarar 1972, sai ya je kasar Hong Kong sau biyu a cikin kwane makwanni biyu domin ya sayo kayan masarufi, saboda ba su a birnin Beijing na kasar Sin. Ba zai iya samun Suga, Madara, Cornflakes a Beijing ba, sai ya je Hong Kong a shekarar 1972 fa, ba wai shekaru 100 a baya ba.

“A shekarar 1974 ne, Deng Diaoping, ya fara bude wa kasar Sin ido, a lokacin akwai sama da mutanan kasar na Sin milyan 700 da suke rayuwa a cikin katutun talauci. Maganan da muke yi a yau din nan, wannan adadin sun dawo kasa da milyan 30, a cikin fa zamani guda daya tal. A shekarar 1974, kasar Sin tana da wadanda suka kammala karatun digiri milyan takwas ne kacal. A yanzun, kasar Sin tana da sama da dalibai milyan 300 da suka kammala karatun su na digiri, watau sama da yawan al’ummar kasar Amurka kacokam. Duk da hakan, kasar ta Sin ba ta da hannun jari na kai tsaye a wajen ta, kai ta ma dakatar da yin hakan ne.

“Muna ta maganan abin al’ajabi. Ba na son fadin wannan kalmar ta al’ajabi, saboda al’ajabi yana da dangantaka ne da kila mala’iku masu fikafikai wadanda ba ma iya ganin su da idanuwanmu, masu sauka daga sama. Mutanan kasar Sin ‘yan adam ne kamar mu, su din ne kuma suka iya canza kasar su haka. Bambancin da ke tsakaninmu da su kawai shi ne, irin tsarin da muke gudanarwa.

“Za mu yi babban zabe a 2019, a kullum ina karanta jaridu, ina kuma kallon talabijin, ina sauraron duk abubuwan da ake tattaunawa, a cikin ‘yan siyasan, wa ke yin maganan ilimi? Wa ke yin maganan lafiyayyen abinci? Wa ke yin maganan samar da kyakkyawan tsarin lafiya? A matsayinmu a nan kasar, wadanne abubuwa ne muka fi bukata? Ba mu da isassun kudin da za mu bayar da nagartaccen ilimi.

“Ba mu da isassun kudin da za mu inganta tsarin lafiyarmu. Ba mu da isassun kudin da za mu samar wa da kanmu lafiyayyen abinci. Amma muna da Naira triliyan daya ko ma biyu da za mu kashe a tallafin mai. Ina hankalin mu ne ya tafi na tsayawa mu duba abubuwa masu mahimmanci a gare mu, ina kuma jarin da muke zuba wa zuriyar mu?

“Ba wanda ya damu da makomar wannan kasar, babban aikin da ke gaban mu shi ne mu tabbatar da cewa ba mu mayar da wannan kasar shalkwatar matalautan duniya ba a nan da shekaru 30 masu zuwa.

“Cewa muke yi muna da arzikin man fetur, saboda mun manta da lissafi mai saukin fahimta. Kasar Saudiyya ita ma tana da arzikin man fetur, saboda a kullum tana fitar wa da duk ‘yan kasar ta uku gangar mai guda. Suna fitar da gangar mai milyan goma, sa’ilin da yawan su kwata-kwata su milyan 30 ne a kasar. A Nijeriya muna fitar da gangar mai milyan biyu ne kacal, alhalin muna da al’umma mai yawan milyan 200,” in ji Sarki Sanusi.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment