Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba ya bayyana cewa tsakaninsa da Mourinho biyayya ce kawai kuma kawo yanzu babu wani abu da yake tsakaninsu mara dadi.
Pogba ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai inda ya karyata rade radin da akeyi na cewa zai bar kungiyar ta Manchester United a karshen wannan kakar sakamakon rashin jituwar da yake tsakanisa da mai koyar da kungiyar.
An bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa ce tafara zawarcin dan wasan dan kasar Faransa domin yakoma kungiyar da buga wasanni inda itama kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen aka bayyana cewa tafara zawarcin dan wasan.
Sakamakon rashin jituwar dai yasa mai koyar da ‘yan wasan kungiyar ya ajiye Pogba a wasan da kungiyar ta buga da kungiyar Sebilla a gasar zakarun turai sannan kuma a wasu wasannin kungiyar Mourinho ya ajiye Pogba a benchi.
Sai dai Pogba yace daman dole a matsayinsa na dan adam kuma a matsayin dan wasa da mai koyarwa watarana za’a samu rashin fahimtar juna domin watarana dan wasa zai iya ganin wani abin shine dai-dai mai koyarwa yace ba haka ba ko kuma mai koyarwa yace abu shine dai-dai dan wasa yace ba haka ba.
Ya kara da cewa yana farin cikin saka rigar Manchester United domin a shekarun baya ya bugawa kungiyar yana matashin dan wasa yanzu kuma ya buga yana babban dan wasa kuma kwararre wanda aka siya da tsada.

![[Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So [Music]: Snow_White_Ft_Rocxeey-Ke-Nike-So](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYYQvKACERNZ4Y9r0zSC-Qn8AP552jWu2Zq6zLs9m8uem6wDDygjcZPXfmkaTO9Wg2CDNmU3PLt4LwQyVvgXxSqZZFhZ5gaozQA8equvRaFXqzMOw7diVPhalEpyUCynEC1mvaiwCVvHQ/w100-h100-p-k-no-nu/IMG-20181023-WA0000.jpg)