olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

Yan Wasa 10 Zasu Bar Manchester United Idan Ba'a Kori Mourinho Ba!!



Wasu rahotanni da suke fitowa daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana tunanin ‘yan wasa kusan guda goma za su bar kungiyar idan har Mourinho yaci gaba da zama a kungiyar.

Mai koyarwa Jose Mourinho dai baya shiri da wasu dayawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar dalilin kennan dayasa kungiyar bata buga abinda akeso a wannan kakar sakamakon rikicin daya dabai baye kungiyar.

Nasarar da kungiyar tasamu akan Newcastle United a ranar Asabar din data gabata shine yasa kungiyar ta farfado daga halin datake ciki sai dai duk da wannan nasarar wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar suna ganin baza su iya cigaba da zama da Mourinho ba

Rashin jituwa tsakanin dan wasan kungiyar dayafi tsada Paul Ppgba da Mourinho shine wanda yafi jan hankalin mutane kuma tuni aka bayyana cewa Pogba ya shirya barin kungiyar a watan Janairu ko karshen kakar wasa.

Kwantaragin dan wasa Luke Shaw zai kare a karshen wannan kakar kuma abune mai wahala dan wasan ya sake sabon kwantaragi indai Mourinho zaici gaba da zama a kungiyar yayinda mai tsaron raga Dabid De Gea da Anthony Martial ma suke son tafiya indai Mourinho zaici gaba da zama.

Kaftin din kungiyar Antonio Balencia da Eric Bailly da Juan Mata da Ander Herrera da Ashley Young da Phil Jones duk suma kwantaraginsu zai kare a karshen wanann kakar.
Related Posts

Related Posts

Post a Comment